Kamfanin Neta na kasar Sin mai kera motoci masu amfani da lantarki, ya shiga kasuwar kasar Kenya, inda ya hada gwiwa da kamfanin Moja EV Kenya mai dilar motoci.
Zhou Jiang, manajan Neta mai kula da harkokin cinikayya a kasashen waje, ya shaidawa manema labarai jiya a babban birnin Nairobi cewa, kamfanin zai fara da gabatar da samfurin motar Neta V, wadda farashinta ta kama shilling miliyan 4, kwatankwacin dala 31,000, dake iya tafiyar kilomita 380 idan aka mata cikakken caji.
A cewar Wang Aiping, babban jami’in Moja EV na Kenya, za su kai motoci 160 kasar daga Sin cikin wata mai zuwa, kuma za su hada gwiwa da masu harhada motoci na kasar Kenya domin hada motoci masu amfani da lantarki guda 250 a duk wata. Ya kuma kara da bayyana shirinsu na fitar da motocin na kasar Sin daga Kenya zuwa sauran sassan nahiyar Afrika.
Ya ce motoci masu amfani da lantarki na da fifiko, inda suke dogaro da batura, ga kuma rashin inji mai sarrafa fetur, lamarin dake rage bukatar kai su wurin gyara akai-akai. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)